ABNA24 : Lamarin dai ya faru ne a cikin daren Lahadi wayewar safiyar Litini, yayin da sojojin suka murkushe wani wunkurin kungiyar boko haram na kai hari kan sansanin sojin Chetima Wongo, a cewar wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar, kamar yadda gidan radiyon faransa na rfi, sashen faransanci ya nakalto.
Baya ga sojojin hudu da suka rasa rayukansu da akwai da dama da suka jikkata wanda yanzu haka suke karbar magani.
342/